News
Kotu A Kano Ta Yanke Wa Matasa Biyu Daurin Watanni Shida Kan Laifin Sojan Gona Da Sunan Ma’aikatan EFCC.
Wata babbar kotu da ke Kano ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Nasiru Saminu ta yanke wa matasa biyu hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari kan laifin kwaikwayon jami’an Hukumar EFCC domin yaudarar jama’a.
Matasa biyu da aka yankewa hukuncin su ne Buhari Abdullahi da Umar Mukhtar Usman.
Kwamishinan Sufuri Na Kano Ya Janye Daga Karbar Belin Wanda Ake Zargi Safarar Miyagun Kwayoyi
A cewar wata sanarwa da Hukumar EFCC ta fitar a ranar Jumu’a, 25 ga Yuli, 2025, ta ce lamarin ya faru ne a watan Mayu na wannan shekara.
Sanarwar ta ce mutanen biyun sun bayyana kansu a matsayin jami’an bincike na hukumar EFCC tare da amfani da katin shaidar bogi domin su damfari jama’a.
Bayan gurfanar da su a gaban kotu, sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi.
Lauyan EFCC, Idris I. Haruna, ya gabatar da hujjoji tare da roƙon kotu da ta yanke musu hukunci bisa amsa laifin da suka yi.
Mai shari’a Nasiru Saminu ya yanke hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ga kowannen su, tare da zabin biyan tarar naira dubu hamsin (₦50,000).
Hukumar EFCC ta ce za ta ci gaba da bibiyar irin waɗannan masu kwaikwayon jami’anta, tare da bukatar jama’a su rika ba da hadin kai wajen tona masu irin waɗannan laifuka.
-
News1 day ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
