News
Yakin Ukraine: An rusa kusan gine-gine dubu a birnin Kharkiv
Daga Yasir sani abdullahi
Bari kuma mu koma kan yaƙin da ake gwabzawa a yankin arewa maso gabashin Ukraine, a birnin Kharkiv wanda Rasha ke wa ruwan bama-bamai.
Kusan gine-gine 1,000 aka yi raga-raga da su a sanadin bama-baman da Rasha ke jefa wa birnin daga wajensa, kamar yadda hukumar da ke kula da ayyukan jin kai ta Ukraine ta sanar.
Yawancin gine-ginen da aka rusa gidajen zama ne.
Dakarun Rasha sun sa birnin a gaba, inda babu ƙaƙƙautawa suke harba bama-bamai kan birnin, wanda ke da nisan kilomita 30 daga kan iyakar Ukraine da Rasha.
Akalla fararen hula 500 aka kashe, kamar yadda jami’an kasar Ukraine ke cewa.
Advertisements
