Connect with us

News

Yan Sanda Sun Kama Mace Bisa Zargin Satar Adai-daita Sahu a Jigawa

Published

on

download (2)

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta cafke wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a sassa daban-daban na jihar, ciki har da wata matashiya da ake zargi da satar babur mai ƙafa uku (adai-daita sahu).

Kakakin rundunar, DSP Lawan Shi’isu Adam, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce jami’an ‘yan sanda sun kama wata mace mai shekaru 21 tare da wani mai suna Nazifi Ahmed bisa zargin sace adai-daita sahu a yankin Dutse.

Advertisement

Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Uwa Da Suka Yi Garkuwa Da Kansu Don Karɓar Miliyoyin Kuɗi A Abuja

“Binciken farko ya nuna cewa wadanda aka kama na da hannu a sace babur mai ƙafa uku, kuma yanzu haka ana ci gaba da zurfafa bincike don gano sauran abokan aikinsu,” inji DSP Shi’isu.

Baya ga haka, rundunar ta kuma kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. An kama su ne tare da kayan maye da wasu makamai masu haɗari.

Advertisement

DSP Shi’isu ya ƙara da cewa rundunar ba za ta sassauta ba wajen cigaba da yaki da masu aikata laifuka a jihar, tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen dakile laifuka a cikin al’umma.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

HIKIMA RTV

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending