News
Dalilan da Suka sa Gwamnonin Najeriya Ke Kin Sanya Hannu a Takardun Hukuncin Kisa
Yawancin gwamnonin jihohin Najeriya na nuna jinkiri wajen sanya hannu a takardun hukuncin kisa saboda dalilai da dama masu sarƙaƙiya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa hakan ba zai rasa nasaba da wasu dalilai na imani da kuma aƙidun addini ba.
Jami’an NSCDC Sun Kama Wani Da Ake Zargi Da Dillancin Miyagun Kwayoyi A Kano
Masana na cewa akasarin gwamnonin suna da tasirin ra’ayoyinsu na ƙashin kai, inda addinin Kiristanci da na Musulunci duka ke jaddada jinƙai da gafara.
Binciken NAN a jihohin Kaduna, Kano da Katsina ya nuna cewa hakan na sanya gwamnonin ƙin amincewa da aikewa da waɗanda kotu ta yanke wa hukuncin kisa.
Haka zalika, wasu gwamnonin na jin tsoron kuskuren yanke hukunci da kotu ka iya yi.
An sha sukar tsarin shari’a a Najeriya saboda jinkiri, raunin bincike da rashin samun ƙwararrun lauyoyi da ke kare mutane yadda ya kamata — al’amuran da ke haifar da shakku game da yiwuwar yanke hukuncin da bai dace ba.
Wasu daga cikin gwamnonin kuma suna jinkirin sanya hannu ne saboda dalilai na siyasa, ganin cewa sanya hannu a hukuncin kisa na iya haifar musu da matsala da masu jefa ƙuri’a ko ƙungiyoyin da ke adawa da hukuncin kisa.
Sauran gwamnonin na ganin cewa hakan na iya jawo musu suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da ƙungiyoyin addini.
Haka kuma, tsawon lokacin da ake ɗauka wajen ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara har ma da kotun ƙoli, wanda ke ɗaukar shekaru, na daga cikin dalilan jinkirin. Waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa na da damar ɗaukaka ƙara, lamarin da ke sanya gwamnonin zama masu taka tsantsan.
Haka kuma, kasancewar Najeriya na cikin ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyoyin kare haƙƙin ɗan adam da ke sukar hukuncin kisa, na iya shafar hukuncin da gwamna zai yanke.
Waɗannan dalilai duka sun haifar da wani yanayi na jinkirin aiwatar da hukuncin kisa, inda dubban fursunoni da aka yanke wa hukuncin ke zaman jiran mafita.
Wasu masana da ƴan ƙasa na kiran a sake duba tanadin kundin tsarin mulki, inda suke ganin ya kamata kotuna su riƙa sanya hannu a takardun hukuncin kisa maimakon gwamnonin.
Farfesa Yahaya Bunkure daga Sashen Ilimin Kimiyya na Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga tanadin kundin tsarin mulki na Sashe na 212, wanda ya ba gwamnonin jihohi damar bayar da izini kafin aiwatar da hukuncin kisa da kotu ta yanke.
Wasu mutane na zargin cewa wasu gwamnonin na jinkiri wajen sanya hannu a takardun hukuncin kisa ne saboda cin hanci da rashawa, duk da cewa tsarin mulki ya basu wannan dama.
