News
Ministocin Ghana Uku Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Sama
Wasu ministoci uku na gwamnatin Ghana sun rasu a wani hatsarin jirgin helikwafta da ya faru a ranar Laraba, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Cikin wadanda suka rasa rayukansu har da Ministan Tsaro Edward Omane Boamah, Ministan Muhalli, Kimiyya da Fasaha Ibrahim Murtala Muhammed, da wasu jami’an gwamnati hudu tare da wasu sojoji uku da ke cikin jirgin.
Dalilan da Suka sa Gwamnonin Najeriya Ke Kin Sanya Hannu a Takardun Hukuncin Kisa
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Julius Debrah, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Accra, inda ya ce hatsarin ya girgiza kasar baki ɗaya.
“Shugaban kasa John Mahama da gwamnatin Ghana na mika sakon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu – ’yan siyasa da jami’an tsaro da suka mutu a yayin hidima ga kasa,” in ji Debrah.
Hukumomin kasar ba su bayyana musabbabin hadarin ba a yanzu, sai dai rundunar sojin saman Ghana ta ce an daina jin duriyar jirgin saman nau’in Z9 a radarsu kafin daga bisani aka tabbatar da hatsarin.
