Connect with us

News

Kano: Makaranta Ta Maye Gurbin “Sign Out” Da Bikin Yaye Dalibai Mai Cike Da Ilmantarwa Da Fadakarwa

Published

on

screenshot VID 20250816 WA0012 1755353242061

Wata makaranta a unguwar Kurna Asabe, mai suna Maahad Abdullahi College of Qur’anic Studies, ta sauya tsarin al’adar da aka saba gani a tsakanin daliban sakandare na yin “sign out” bayan kammala jarrabawa, inda ta maye gurbin hakan da bikin yaye dalibai mai ɗauke da shirye-shiryen ilmantarwa da fadakarwa.

Rahotanni na nuni da cewa an ɗauki wannan mataki ne domin kawar da dalibai daga abin da suka kira “ta’ada ta rashin daidai”, wato barnar dukiya da ake yi ta hanyar zane jikin kayan makaranta, rubuce-rubuce marasa amfani da sauran ayyuka da ba su da alfanu.

Advertisement

Sojin Najeriya Sun Rusa Gidaje A Kaduna Duk Da Umarnin Kotun Jihar

A maimakon haka, makarantar ta shirya taron yaye dalibai da ya ƙunshi jawaban ilmantarwa daga malamai, tunatarwa kan darajar ilimi, gabatar da shirye-shiryen nishaɗantarwa masu ma’ana da kuma girmama dalibai da suka yi fice.

Wannan tsari ya ja hankalin iyaye da al’umma, inda da dama suka yaba da irin wannan salon da makarantar ta kirkira, suna mai cewa hakan zai taimaka wajen ɗora dalibai a kan turbar tarbiyya da gyaran halayya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending