News
An kama mutum 288 kan zargin tayar da hargitsi a zabukan cike gurbi a Kano
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama mutum 288 bisa zargin tayar da hargitsi a yayin da ake gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu mazaɓu na Jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Kano: Makaranta Ta Maye Gurbin “Sign Out” Da Bikin Yaye Dalibai Mai Cike Da Ilmantarwa Da Fadakarwa
Ya ce mutanen kama suna ɗauke da muggan makamai, ciki har da bindigogi da aka yi a gida da wuƙaƙe da adda da sauransu.
A ranar Asabar ɗin nan ne ake gudanar da zaɓukan cike gurbi a mazaɓu goma sha shida a jihohi 13 – Adamawa, Anambra, Edo, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Neja, Ogun, Oyo, Taraba da Zamfara.
Sai dai fafatawar tana yin zafi a jihohi irin su Kano da Kaduna sakamakon mummunar adawar da ke tsakanin wasu manyan ‘yan siyasar jihohin.
A Jihar Kano inda Jam’iyyar NNPP take mulki, an ja zare tsakaninta da Jam’iyyar APC wadda aka kayar a zaɓen shekarar 2023.
