Connect with us

News

Shugabannin Siyasa Ne Ke Hura Wutar Fadan Daba A Kano — Barista Abba Hikima

Published

on

Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano

Wani lauya a Kano, Barista Abba Hikima, ya bayyana cewa shugabannin siyasa ne ke hura wutar rikicin daba da ake ta fama da shi a birnin Kano.

Hikima ya yi wannan jawabi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya jaddada cewa Shugabannin siyasa ne ke hura wutar fadan daba a Kano.

Advertisement

An Cafke Matashin Da Ya Yi Garkuwa Da Kansa Domin Karɓar Kuɗin Fansa Daga Hannun Iyayensa.

A nasa bangaren, Comrade Salisu Gambo Ditol, ya yi fashin baƙi kan lamarin ya ce rashin tsari da rashin gaskiya daga shugabannin siyasa ke haddasa yadda matasa ke fadawa cikin ayyukan tada zaune tsaye.

Ya ce, a mafi yawan lokuta, ’yan siyasa kan rika amfani da matasa wajen cimma muradunsu na siyasa, sannan daga bisani su barsu cikin kangin rashin aikin yi da rashin kulawa, abin da ya kara dagula zamantakewar al’umma.

Advertisement

Ditol ya bayyana cewa ya kamata ’yan siyasa idan za su yi yawon  siyasa, su rika tafiya da ’ya’yansu.

A cewarsa, hakan zai tabbatar da cewa suna shirye da gaske wajen magance matsalolin da matasa ke fuskanta a Najeriya.

Advertisement

Ditol ya kara da cewa, “Yawan zubar da jini da tashin hankali da ake fuskanta ya samo asali daga rashin tsaro da rashin adalcin shugabanninmu. Don haka lokaci ya yi da za a tilasta ’yan siyasa su dauki alhakin gyara halin da matasa ke ciki.”

Ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su yi duba mai zurfi wajen samar da hanyoyin da za su kawo karshen wannan matsala, domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar Kano dakasa baki daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending