Connect with us

News

‘Yan Nijeriya Sun Biya Naira Biliyan 2.57 A Matsayin Kuɗin Fansa A Shekara Ɗaya – Rahoto

Published

on

Wani sabon rahoto da kamfanin binciken tsaro na SBM Intelligence ya wallafa ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya sun biya Naira biliyan 2.57 (kimanin dala miliyan 1.66) ga masu garkuwa da mutane tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni 2025.

Rahoton mai taken “The Economics of Nigeria’s Kidnapping Industry” ya ce masu garkuwa sun buƙaci kuɗin fansa da ya kai Naira biliyan 48, amma abin da suka samu bai kai haka ba. Duk da haka, rahoton ya nuna cewa wannan sana’ar ta garkuwa da mutane ta zama wata hanyar samun kuɗaɗen shiga ga ƙungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka, inda suke amfani da kuɗin wajen siyan makamai, horas da sabbin mutane, da kuma ƙarfafa dabarunsu.

Advertisement

Faifen Bidiyon Dala: Tsohon Kakakin Ganduje, Ya Janye Shaidarsa Kan Ja’afar Ja’afar

Rahoton ya ce akalla mutane 4,722 aka yi garkuwa da su a wurare 997 a fadin ƙasar a cikin wannan lokaci, yayin da aka kashe mutum 762 a hare-haren da ke da nasaba da garkuwa.

Yankin Arewa maso Yamma ne ya fi fama da wannan matsala, inda aka samu rahoton wurin 425 (42.6%) na garkuwa da mutane, kuma mutane 2,938 (62.2%) aka yi garkuwa da su daga yankin.

Advertisement

Jihar Zamfara ce ke kan gaba da mutane 1,203 da aka yi garkuwa da su, sai Kaduna da Katsina.

Rahoton ya ce yankin Kudu maso Yamma ne ya fi ƙanƙanta da rahoton garkuwa da mutane, inda ya tsaya a kashi 5.3% na hare-haren, kuma kashi 3% na waɗanda abin ya shafa

Advertisement

SBM ta bayyana cewa garkuwa da mutane ya koma kamar tsarin kasuwanci a tsakanin ‘yan ta’adda, inda suke amfani da hanyoyin sadarwa, yarjejeniya da kuma raunin tsaro na ƙasa wajen gudanar da wannan mugun aiki.

A cewar rahoton, a shekarar 2022, masu garkuwa da mutane sun karɓi N653.7m a matsayin kuɗin fansa (kimanin dala $1.13m). Amma a shekarar 2025, kudin ya haura zuwa Naira biliyan 2.57, abin da rahoton ya danganta da hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar naira.

Advertisement

Rahoton ya kuma nuna cewa an fi buƙatar manyan kuɗaɗe daga Kudu maso Kudu, inda aka nemi kuɗin fansa har Naira biliyan 30 a jihar Delta. Sai kuma Arewa maso Gabas da ta fi biyan kuɗin fansa da aka tabbatar, inda aka biya Naira miliyan 766 wajen sakin Mai Shari’a Haruna Mshelia daga hannun Boko Haram.

Duk da hare-haren sojoji da ‘yan sanda, rahoton ya nuna cewa waɗannan farmakin ba su dawwama. Haka kuma, shirin gwamnati na hana biyan kuɗin fansa ya ci tura, domin iyalai kan yi biyan don ceto ‘yan uwansu saboda rashin wani zaɓi.

Advertisement

Kamfanin SBM ya yi kira da a samar da tsare-tsaren da za su haɗa ingantaccen tsaro, leƙen asiri daga matakin al’umma, da kuma tallafi na tattalin arziki, tare da ƙara tsaurara matakan bibiyar yadda ake tafiyarda kuɗaɗen fansa a ƙasar.

 

Advertisement

 

TRT GLOBAL

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending