News
Masu Sa Kai Sama Da 9,600 Za Su Taimaka Wajen Rijistar Masu Kada Kuri’a A Kano
Kwamitin Wayar da Kan Jama’a kan Rijistar Masu Kada Kuri’a a Kano ya ce sama da masu sa kai 9,680 za su shiga aikin rijistar kuri’a ta yanar gizo a kananan hukumomi 44 na jihar.
An shirya tura aƙalla masu sa kai 20 da na’urorin Android a kowace gunduma, bisa la’akari da yawan rumfunan zaɓe a yankin.
An Kama Uba da Ɗansa Bisa Zargin Cin Zarafin ’Yar Shekara 13 A Gombe
Wannan na cikin matsayar da aka cimma a taron da kwamitin ya yi da shugabannin kananan hukumomi a dakin taro na Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta a ranar Litinin.
Kwamitin ya ce za a horas da duk masu sa kai kan yadda ake yin rijistar ta yanar gizo kafin su fara aiki. Haka kuma, za su horar da wasu masu sa kai a matakin rumfunan zaɓe domin tabbatar da nasarar shirin.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce taron ya yi nufin haɗa kai da shugabannin kananan hukumomi don ganin jihar ta samu ci gaba wajen rijistar masu zabe.
Ya ce sakamakon rijistar da aka gudanar a baya ya nuna ƙarancin shiga daga Kano duk da cewa ita ce mafi yawan jama’a a Najeriya.
Kwamared Waiya ya tabbatar da cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuduri aniyar samar da dukkan kayan aiki da tallafi don tabbatar da nasarar aikin.
A nasa jawabin, Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Alhaji Muhammad Tajo Othman Zaura, ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da su kara kaimi wajen wayar da kan jama’a.
Shugaban karamar hukumar Nasarawa kuma mataimakin shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa (ALGON), Alhaji Yusuf Imam Ogan Boye, ya tabbatar da shirin shugabannin kananan hukumomi na ganin aikin ya samu nasara.
Kwamitin daga bisani ya gana da kansiloli 484 a fadar gwamnatin Kano, inda Waiya ya nemi cikakken goyon bayan su.
Shugaban Kungiyar Kansiloli, Alhaji Bashir Achika, ya ce aikin rijistar kuri’a muhimmin mataki ne a tsarin zabe, ya kuma tabbatar da cewa za su bayar da cikakken goyon baya.
