News
KANO: Jami’an Yan Sandan Sun Kama Mutane 9 Kan Tarzomar Da Ta Faru A Garko.
Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane tara da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke a karamar hukumar Garko, wanda ya haddasa konewar motoci, raunata jami’an tsaro, da kuma mutuwar mutum ɗaya. Rundunar ta kuma ce tana ci gaba da bincike kan zargin kisan kai da ya faru a yankin.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Asabar, an bayyana cewa lamarin ya samo asali ne daga kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wani mai babur a Garko. An kai su ofishin ’yan sanda na Division domin bincike, sai dai gungun jama’a dauke da duwatsu da sanda sun kai farmaki a ofishin suna neman a mika musu wadanda ake zargin.
Sanarwar ta ce cikin arangamar ne aka kone motar sintiri ta ’yan sanda, tare da lalata motocin Hisbah guda biyu da na Garko Local Government Council, da kuma farfasa tagogin ofishin ’yan sanda. Rundunar ta ce jami’anta uku sun ji raunuka kuma an garzaya da su asibitin Wudil, inda suke karɓar magani.
Haka kuma, a lokacin tashin hankali, wata tayar mota da aka kunna ta fashe ta kuma bugi ɗaya daga cikin masu tayar da zaune-tsaye, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa, yayin da wasu uku suka ji raunuka. Lamarin ya kara tayar da hankulan jama’a a yankin.
Rundunar ta gargadi jama’a da su daina ɗaukar doka a hannunsu, tana mai cewa hakan na kawo cikas ga doka da oda. Ta kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da adalci.
