News
Kotu ta yanke hukuncin daurin shekara guda a gidan gyara hali

Daga maryam bashir musa
Kotu ta yanke hukuncin daurin shekara guda a gidan gyara hali ga lauyan bogin da ya je ofishin hukumar EFCC kwanakin baya karbar belin wani wanda ake tuhuma da almundahana.
Hukumar ta kuma gurfanar da mutumin mai suna Emmanuel Adekeye Adekola a gaban kuliya a jihar Legas.
Bayan watanni biyu ana shara, Alkalin kotun ta yankewa mutumin daurin shekara guda a gidan gyara hali.
A watan Junairu, hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzkin kasa zagon kasa watau EFCC ta damke lauyan bogi, Adekola
Adekeye, kan laifin kirkiran takardun bogi don damfara. Kakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce asirin lauyan ya tonu ne lokacin da yaje ofishin hukumar karban belin wani dan damfara.
