Connect with us

News

Rashin Shugabanci Na Gari Shi Ne Asalin Matsalar Najeriya — Sarkin II

Published

on

Former Emir of Kano Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa Najeriya ta shafe dogon lokaci tana fama da shugabanni marasa nagarta, abin da ya ce shi ne tushen matsalolin da ake ci gaba da fuskanta a ƙasar.

Sanusi ya yi wannan magana ne a Kano, yayin bikin Kano International Poetry Festival da aka gudanar a ranar Asabar.

Advertisement

Yan Bindiga Sun Bude Wa ‘Yan Zaman Makoki Wuta

Ya ce ci gaban kowace ƙasa yana ta’allaka ne da ingancin shugabanci, amma Najeriya ta daɗe tana tangal-tangal saboda shugabanni waɗanda suka kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

“Kowace rana kuna gani a jaridu da labarai, ’yan majalisa suna ɓata lokaci kan abubuwan da ba su da amfani, yayin da sauran ƙasashe suke tattauna kan sauyin yanayi da fasahar zamani. Amma mu har yanzu muna gardamar kan ƙabilanci da addini kamar yadda aka yi tun shekarun 1960,” in ji shi.

Advertisement

Sanusi ya yi kira ga matasa da su ɗauki ragamar shugabanci daga hannun tsofaffin da suka shafe shekaru suna mulki.

Sarkin ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta ɗauka. Ya ce tallafin bai amfanar da Najeriya ba, illa dai ƙara ciyar da masana’antun ƙasashen waje gaba, maimakon a gyara na cikin gida.

Advertisement

“Da biliyoyin da aka kashe wajen biyan tallafin man tun 2012 aka saka a gyaran matatun mai, da yanzu Najeriya ta fi haka,” in ji shi.

Sanusi ya yi gargaɗi kan yadda gwamnati ke yawan karɓar bashi da kuma ɓatar da shi ba tare da an mayar da shi ga ayyukan raya ƙasa ba.

Advertisement

Ya ce irin wannan dabi’a na iya jefa tattalin arziƙin Najeriya cikin mawuyacin hali a nan gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending