News
Yan Bindiga Sun Bude Wa ‘Yan Zaman Makoki Wuta
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, ta fara bincike kan kisan wasu mutum huɗu da ’yan bindiga suka yi lokacin da suke zaman makoki.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa masu makokin wuta ne a ranar Alhamis a garin Ogidi, da ke Ƙaramar Hukumar Idemili.
Masu Zuwa Daurin Aure 19 Sun Rasu Bayan Rushewar Gada A Zamfara
Harin ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu tare da jikkata aƙalla mutum 15.
Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga, ya ce suna zargin harin ya shafi rikicin ƙungiyoyin asiri ne.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da suka isa wajen sun gano harsasai 16, kuma za su yi amfani da su wajen bincike.
Ikenga, ya ce nan gaba za su sanar da jama’a abin da binciken nasu ya gano.
Advertisements
