News
Limamin Masallacin Juma’a ya ajiye limanci sabo da zai tsaya takara a Katsina
Daga maryam bashir musa
Imam Muhammad Hashim, Limamin Babban Masallacin Juma’a na GRA a Jihar Katsina ya ajiye muƙamin limancin sabo da zai tsaya takara.
A wasiƙar ajiye limancin da ya rubuta, mai ɗauke da kwanan watan 24 ga Maris, Mallam Hashim ya yi addu’ar Allah Ya rubuta masa ayyukan alherin da ya yi a cikin ayyukansa.
Wani ɓangare na wasiƙar, wacce Daily Nigerian Hausa ta gani ya ce, ” Ni Muhammad Hashim (Liman) na aje muƙami na na limancin Babban Masallacin Juma’a na GRA sabo da tsayawa takara da zan yi.
“Ina fatan Allah SWT Ya rubuta mana ayyukan mu na alheri a cikin ibadun mu da mu ka gabatar, Ya yafe mana kusa-kuren mu Amin.
A cikin wasiƙar, mai ɗauke da sa hannunsa, Hashim ya nemi yafiyar ƴan kwamitin masallacin da ma al’umma baki ɗaya.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
