Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa Ta Shafi Kauyuka 13 A Adamawa

Published

on

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) reshen Yola ta jagoranci aikin ceto bayan ambaliyar ruwa ta afkawa ƙauyuka 13 da ke cikin ƙananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu a jihar Adamawa.

Shugaban ayyukan NEMA a Yola, Ladan Ayuba, ya ce tawagogin gaggawa daga hukumar ADSEMA, jami’an kashe gobara na jiha da na tarayya tare da masu aikin sa-kai, sun shiga cikin gaggawa domin ceto jama’ar da ambaliyar ta rutsa da su.

Wani Mutum Ya Rasu Yayin Da Yake Ƙoƙarin Raba Faɗan Ma’aurata 

Ya bayyana cewa an kwashe mata, yara, tsofaffi da masu nakasa daga yankunan da ke cikin haɗari zuwa sansanonin wucin-gadi da wuraren da suka fi aminci. A cewarsa, bincike na ci gaba da gudana domin gano girman illar ambaliyar, hasarar dukiya da gine-gine, da kuma irin bukatun agaji na gaggawa.

“Aikin ya gudana ne cikin haɗin gwiwa da hukumomin jihar Adamawa, ƙananan hukumomi, jami’an tsaro da ƙungiyoyin agaji, domin tabbatar da cewa jama’a sun samu taimako cikin lokaci,” in ji Ayuba.

Ya kuma tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon ambaliyar.

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending