News
Magidanta Na Fargabar Farashin Kayan Masarufi Gabanin Ramadana
Daga sani abbas sani
A lokacin da ake gab da fara azumin watan Ramadan, ‘yan kasuwa da magidanta na fatan ganin farashin kaya ya sauka don samun sauki ga masu saye da sayarwa.
Sau tari magidanta na shiga zullumi da fargaba musamman idan lokacin bukukuwa na tunkarowa, kamar bikin sallah ko zuwan watan Ramadana ko kuma bikin kirsimeti, sakamakon yadda kayan masarufi ke tashin goron zabi.
Hakan yasa a dukkan lokacin da watan Ramadana ya karato, mutane kanyi tanadi abinda ya shafi cimaka da sauran abubuwan bukatu tun kafin lokacin.
Kayan Marmari Abinci
Muryar Amurka ta ziyarci kasuwar FCDA dake Babban birnin tarayya Abuja inda ‘yan kasuwar suka shaida cewa tashin bai taka kara ya karya ba kuma suna fatan a kara samun saukin farashin kayan.
Akan bukaci kayan marmari da dabino a lokacin azumi hakan yasa tuntubi Malam sabo Mai dabino don ji ta bakin sa, inda ya bayyana cewa kayayyakin sunyi tsada.
Anfi danganta faruwar wannan al’amari ga ‘yan kasuwa, kan tsauwalawa kayan masarufi da kayan cimaka da sauran abubuwan bukata.
Sai dai Asifu dake kasuwar FCDA yace yadda suka samo kayan haka suke kasawa.
A bana ma magidanta asun koka game da yadda kayan masarufi ke kara kudi, suna masu kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su duba al’amarin
Saidai wasu na dora alhakin akan gwamnati data kasa tsaida kyakykyawan farashi wadda yake da ka’ida.
-
News7 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
