Connect with us

News

‎FUDMA Ta Yi Bikin Kaddamar Da Dalibai 1,000 Da Sanata Barau Ya Dauki Nauyin Karatunsu

Published

on

1758604211448

Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), a Jihar Katsina, ta gudanar da bikin kaddamar da dalibai 1,000 da suka samu tallafin karatun digiri daga shirin tallafin ilimi na Sanata Barau I. Jibrin, CFR, FCNA, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

‎Bikin ya gudana a harabar jami’ar ranar Litinin tare da halartar manyan baki, ciki har da Shugaban Hukumar Ci gaban Arewa maso Yamma (NWDC), Farfesa Abdullahi Shehu Maaji; Shugaban Ma’aikatan ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah; da Hajiya Yardada Maikano Bichi, mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin mata.

Advertisement

Yadda Wasu Yan Nijeriya Suka Yi Kashin Ƙulli 116 Na Hodar Ibilis A Gaban Jami’an NDLEA

‎Sanata Barau ya bayyana cewa shirin tallafin, wanda ke gudana karkashin Barau Ibrahim Jibrin Foundation (BIJF), ya kasance wani ginshiki wajen bunkasa ilimi ga matasa daga Kano da sauran sassan Najeriya. Ya ce a halin yanzu, sama da ɗalibai 70 na ci gaba da karatun digiri na biyu da na uku a kasashen waje karkashin shirin.

Advertisement

‎A jawabin da ya gabatar ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, Sanata Barau ya gode wa shugabancin jami’ar karkashin mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’a, Farfesa Aminu Ado, bisa hadin kai da jajircewar da suka nuna wajen tabbatar da nasarar shirin.

Advertisement

‎Kungiyar dalibai ta NAKSS (Kungiyar Daliban Jihar Kano ta Kasa), reshen FUDMA, ta karrama Sanata Barau da lambar yabo ta musamman bisa gudummawarsa wajen raya ilimi da ci gaban matasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending