Connect with us

News

Tsoffin Ƴan Sanda Za Su Sake Gudanar Da Babbar Zanga-Zanga A Gaban Majalisar Dokoki

Published

on

Retired Police Officers Protest At NASS 750x430 1

Kungiyar tsoffin ’yan sanda masu ritaya da ke ƙarƙashin tsarin biyan fansho na tarayya (CPS) ta sanar da shirin gudanar da abin da ta kira “Babbar Zanga-Zangar Lumana” a gaban Majalisar Dokokin ƙasa a ranar Litinin mai zuwa.

A watan Yuli da ya gabata, tsoffin ’yan sanda sun yi irin wannan zanga-zanga a Abuja, inda suka nuna rashin jin daɗinsu kan tsarin tarin kuɗin fansho da suke ganin zalunci ne. Sun yi tattaki daga hedikwatar rundunar ’yan sanda zuwa majalisar dokoki, suna rera wakokin gwagwarmaya da riƙe kwalaye masu rubuce-rubuce irin su: “Shekaru 35 na aiki, Naira miliyan 3 fansho? Abin kunya!” da “Muna buƙatar hukumar fanshon ’yan sanda yanzu!”

Advertisement

Dakarun Soji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace

Cif Sufeto Mannir Lawal Zariya (mai ritaya), shugaban reshen Kaduna na ƙungiyar, ya ce mambobin kungiyar na fama da matsananciyar talauci, rashin samun kulawar lafiya, da wahalhalu wajen biyan buƙatun yau da kullum. Wasu ma sun janye ’ya’yansu daga makarantu saboda tsadar rayuwa, har ma da yawaitar mace-macen tsoffin jami’an.

Ƙungiyar ta bayyana cewa wakilai daga jihohi 35 da Babban Birnin Tarayya za su haɗu a majalisar dokoki domin ci gaba da wannan koke, bayan taron ta Intanet da suka gudanar a ranar 22 ga Satumba, inda suka sake jaddada buƙatar ficewar ’yan sanda daga tsarin tarin kuɗin fansho.

Advertisement

Cif Sufeto Lawal ya ce shekaru fiye da 15 kenan suna kai korafi da rubuta takardu ga gwamnati da majalisar dokoki, har ma da gudanar da zaman sauraron jama’a guda uku. Duk da nuna hujjoji da kwatanta fansho da na sojoji da jami’an hukumar tsaron cikin gida, babu wani canji mai ma’ana da aka samu.

Majalisar Dokoki ta Tara ta amince da kudirin cire ’yan sanda daga tsarin tarin kuɗin fansho, amma shirin ya tsaya cak bayan kasa daidaita shi da na Majalisar Dattawa. Duk da alkawarin da aka yi musu a watan Yuli, Cif Sufeto Lawal ya zargi Hukumar Kula da Fansho da ƙoƙarin dakile ficewar, inda ta gabatar da tayin ƙarin kuɗin alawus da inshorar lafiya.

Advertisement

Sai dai ƙungiyar ta yi watsi da tayin, tana dagewa kan cikakken ficewa zuwa tsarin tsohon fansho (DBS), tare da kafa hukumar fansho ta ’yan sanda. Cif Sufeto Lawal ya ce dukkan mambobi daga shiyyoyi shida na ƙasar sun jaddada buƙatar kafa hukumar ta musamman.

 

Advertisement

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending