News
Matsalar Tsaro Ta Tilasta Rufe Makarantu 188 A Jihohi 7 Na Arewacin Najeriya
Bincike da aka gudanar a Najeriya ya bayyana cewa, aƙalla makarantun gwamnati 188 a yankin Arewacin ƙasar sun rufe sakamakon ayyukan ƴan ta’adda, wadanda ke kai hare-hare da hallaka mutane a wurare daban-daban.
Jaridar Daily Trust ta gudanar da binciken, inda ta nuna cewa matsalar ta fi ƙamari a jihohin Benue da Katsina, wadanda ke da makarantun gwamnati 55 da 52, biye da jihar Zamfara mai makarantu 39, da jihar Neja tare da makarantun 30. Haka kuma, jihohin Sokoto da Kaduna suna da makarantun guda shida kowanne.
A cikin makarantun 39 da aka rufe a jihar Zamfara, 20 daga cikinsu makarantu ne na firamare, yayin da 19 kuma na sakandare. Jihar Neja tana da makarantu 18 na firamare da guda ɗaya na sakandare, sai kuma makarantu 11 na ƴaran makiyaya.
Binciken ya nuna cewa, adadin makarantu da aka rufe zai iya zarce wannan, domin rashin tsaro ya hana gudanar da cikakken bincike a wasu daga cikin yankunan da matsalar ta fi kamari.
Wannan bincike ba ya haɗa da jihohin Borno, Yobe, da Adamawa, wanda ke fama da matsalar Boko Haram tun tsawon shekaru 15.
A cikin wannan lokaci, hukumomi sun kafa cibiyoyin horar da dalibai a sansanin ƴan gudun hijira domin bai wa yara damar samun ilimi. Hukumar UNICEF ta bayyana cewa, fiye da yara miliyan 10 suna rashin damar zuwa makarantar firamare, yayin da adadin yaran da ba su zuwa makarantar sakandare ya haura miliyan 8.
Jihohin Katsina, Sokoto, da Kebbi suna cikin jerin manyan jihohi da ke fuskantar wannan matsala, tare da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar Katsina ya kai miliyan 1 da 400,000, Sokoto miliyan 1 da 250,000, sannan Kebbi miliyan 1 da 60,000.
Waɗannan jihohi suna daga cikin yankunan da ake fama da matsalar ƴan ta’adda, wanda ya haifar da rikice-rikicen da ke tasha kauyuka da garuruwa a yankunan.
