News
Jami’an kwastan sun kama mota maƙare da naman jaki da tabar wiwi na N250m a Kaduna
Daga maryam bashir musa
Hukumar hana Fasa-ƙauri ta Ƙasa, wa ce a ka fi sani da Kwastan, a yau Juma’a ta ce ta kama wata mota cike da naman jaki da kuma buhu 12 na yanar wiwi da kudin sa ya kai Naira Miliyan 250 a tsawon wata ɗaya.
Kwantarolan shiyyar “B” da ke Kaduna, Albashir Hamisu ya shaida wa manema labarai cewa an saka kayan ne a cikin buhuhuna 2,348, inda a ka ƙunshe su a ɗauri-ɗauri 126 da kuɗin su ya kai Naira Miliyan N251,701.
Ya ce rundunar shiyyar ta samu nasarar kwace kayaiyaki har 144 daga 24 ga Febrairu zuwa 23 ga watan Maris.
Da ga cikin muggan kayaiyaki da su ka kwace a wannan lokacin, inji kwantarolan, har da kwallon kwayar tramadol 3,700 da kuma kwayar D6 kwali 460.
A cewarsa, sun kama wani haramtaccen magani mai suna D5, wanda masana suka ce ya na aiki iri ɗaya da tramadol, inda su ka mika shi ga jami’an Hukumar yaƙi da sha da Fataucin miyagun klƘwayoyi ta Ƙasa, NDLEA.
Ya ce sun kama su ne a lokacin da jami’an NDLEA ba sa nan, inda ya ƙara da cewa hadin gwiwa tsakanin hukumomin ne ya sanya su ka mika wa hukumar kayayyakin.
