Connect with us

News

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Published

on

DAGA ZUBAIRU M. LAWAL, LAFIA

Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi gargadi ga duk masu zuba sinadarai a cikin ruwa domin kamun kifi, inda ta ce duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Advertisement

Kwamishinan Ruwa da Ci gaban Karkara na jihar, Mohammed Muluku, ya bayyana cewa zubar sinadari a cikin ruwa yana da matukar haɗari ga lafiyar al’umma, domin ruwan na zama tushen sha da sauran ayyukan gida. “Sinadarin kan janyo asarar rayuka kuma yana jefa al’umma cikin mawuyacin hali,” in ji Muluku.

Gwamnatin Kano Ta Haramta Shan Shisha

Muluku ya ce gwamnati ta gina rijiyoyin burtsatse guda 200 a kananan hukumomi 13 na jihar cikin shekaru biyu da suka gabata, domin inganta samar da ruwan sha mai tsafta da tallafawa ci gaban karkara. Haka kuma, an gyara rijiyoyi 300 a kauyuka da birane domin rage matsalar ƙarancin ruwa da ba wa jama’a damar samun ruwan sha mai tsafta.

Advertisement

Kwamishinan ya kara da cewa, a halin yanzu, akwai gidajen ruwa fiye da tara (9) a Awe, Obi, Keana, Lafia, Nassarawa-Eggon, Akwanga, Wamba, Nasarawa, da Toto, wadanda gwamnati ke kula da su. Ya ce gwamnati tana shirin gina sababbi domin biyan bukatar sababbin unguwanni, sai dai matsaloli kamar lalata kayan aiki da satar igiyoyin lantarki da famfo suna rage tasirin ayyukan.

Muluku ya bayyana cewa gwamnati tana haɗin gwiwa da wasu ƙasashen Afirka da Bankin Raya Afirka wajen inganta ruwan sha mai tsafta. “An amince da bayar da sama da naira biliyan 4.4 domin gyara matsalolin gidajen ruwa na Obi, Nassarawa-Eggon da Akwanga. Haka kuma, gwamna Sule ya amince da naira biliyan 1.5 domin ƙarfafa samar da ruwa a Keffi da kewaye,” in ji shi.

Advertisement

A nasa bangaren, Dr. Ibrahim Tanko, Kwamishinan Labarai, Al’adu da Yawon Bude Ido, ya ce ma’aikatarsa ta samar da hanyoyi da dama domin wayar da kan jama’a kan manufofi da ayyukan gwamnati. Ya yi kira ga jama’a da su kula da gidajen ruwa da sauran kayan more rayuwa domin kare su daga masu lalata su.

Tanko ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin Abdullahi Sule ta kuduri aniyar ganin cewa kowa na shan ruwa mai tsafta da lafiya, domin kare jama’a daga kamuwa da cututtuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending