Connect with us

News

‎Kungiyar Bridge Connect Ta Shirya Taron Bunkasa Ilimin ’Ya’ya Mata A Kano

Published

on

IMG 20251019 WA0019

DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN

‎Kungiyar Bridge Connect Africa Initiative ta shirya wani muhimmin taro a Kano domin samar da hanyoyin inganta ilimin ’ya’ya mata, musamman duba da irin kalubalen da wasu daga cikinsu ke fuskanta wajen kammala karatunsu.

Advertisement

Babbar jami’ar da ke kula da ayyukan kungiyar, Hajiya Fatima Aliyu, ta bayyana cewa manufar taron ita ce a tattauna hanyoyin da za a bi domin karfafa wa ’ya’ya mata gwiwa wajen ci gaba da karatu, tare da samar da mafita kan matsalolin da ke hana su kammala ilimi.

Yadda Wani Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Domin Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

‎ “Mun gayyaci masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi domin mu ji daga gare su irin kalubalen da ake fuskanta, sannan mu samar da dabarun da za su taimaka wajen inganta ilimin ’ya’ya mata a jihar Kano,” in ji Hajiya Fatima.

Advertisement

‎A nasa jawabin, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr Ali Haruna Makoda, ya yabawa kungiyar Bridge Connect bisa kokarinta na tallafa wa gwamnati wajen bunkasa ilimi, musamman na ’ya’ya mata.

‎ “Gwamnatin jihar Kano ta dauki matakai na gina sabbin makarantu da gyaran wasu tsofaffi domin kara wa yara mata damar samun ilimi. Muna kuma kira ga iyaye su dinga tura ’ya’yansu mata makaranta domin su amfana da ilimin zamani,” in ji Kwamishina Makoda.

Advertisement

‎Jaridar Indaranka ta ruwaito cewa taron ya samu halartar dalibai mata daga makarantu daban-daban, da kuma wakilan hukumomi da kungiyoyin fararen hula masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending