News
Ma’aurata 136 Sun Kashe Juna Sakamakon Rikici A Cikin Shekaru 4 A Najeriya
Bayanai sun nuna ma’aurata 136 sun rasa rayukansu a sakamakon rikici a tsakaninsu a cikin shekaru huɗu da suka gabata a sassan Najeriya.
Alƙaluman da muka tattara daga rahotannin manyan jaridun Najeriya sun nuna yanayin rikicin ma’aurata a ɗauƙacin shiyyoyin shida da ke faɗin Najeriya.
‘Sai Mun Yi Tafiyar Sama Da Kilomita Biyu Kafin Mu Sami Ruwa’ — Cewar Mazauna Kunshe A Minjibir
Rahotannin sun nuna matsalolin da suke haifar da hakan a tsakanin ma’aurata da ake zaton zamannsu zai kasance mutu-ka-raba, sun haɗa da zargin cin amanar aure, rikicin abinci, rikici kan waya da sauransu.
Wannan al’amari ya rutsa da mata da maza, masu matsayi daban-daban daga shekarar 2021 zuwa 2025, kuma da alamar ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
Alƙaluman sun nuna matan aure ne waɗanda suka fi rasa rayukansu a irin wannan yanayi, inda aka kashe mata 96 cikin 136, wanda kusan ninki ukun adadin mazaje 39 da aka kashe.
Akwai kuma wasu miji da mata da suka yi mutuwar, dai wata amaryar da aka kashe ana daf da ɗaurin aurenta.
