Connect with us

News

Za A Yi Wa Karin Manyan Sojoji 60 Ritaya Bayan Sauke Hafsoshin Tsaro

Published

on

Nigerian Army

Rahotanni sun bayyana cewa sama da manyan jami’an sojin Najeriya 60 masu mukamin Janar za su fuskanci ritayar dole, sakamakon sauye-sauyen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a bangaren tsaron ƙasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami’an da abin zai shafa sun kasance a matakan da ke sama da sabbin hafsoshin da aka nada, don haka za su tafi ritaya bisa tsarin aikin soja.

Advertisement

Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Gudanar Da Aikin Samar Da Makamin Nukiliya

Majiyoyi sun bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na tabbatar da bin ƙa’idojin aikin soja da tsari. Shugaba Tinubu dai ya sauya manyan hafsoshin tsaron ƙasa ne domin ƙarfafa tsaro da inganta tsarin aiki a rundunonin tsaro na ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending