News
Karamar Hukumar Gwarzo Ta Yi Zarra Wajen Nunawa Tare Da Tallata Sana’ar Gargajiyar Hausa A Bikin KANFEST 2025.
Karamar Hukumar Gwarzo ta nuna bajinta da jajircewa wajen raya da kare al’adun Hausawa da sana’o’in gargajiya a yayin bikin KANFEST (Kalankuwa Festival) wanda Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shirya domin farfaɗo da sana’o’in gargajiya da basirar Hausawa.
Gwarzo na daga cikin manyan garuruwan tarihi a Jihar Kano da suka shahara wajen sana’o’in gargajiya kamar saka (saka buli kare), sassaka itace, sarrafawa da kasuwancin rogo da gyada, da kuma fawa (sayar da nama) waɗanda dukkansu suka kasance ginshiƙan tattalin arziƙin Hausawa da rayuwar yau da kullum.
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Cafke Mutumin Da Yayi Garkuwa Da ‘Yayan Dan’uwan Sa A Bauchi
Bikin wanda ya ɗauki kwanaki uku, an gudanar da shi ne a Trade Fair Complex inda dukkan kananan hukumomin jihar 44 suka halarci bikin da nuni na sana’o’insu. A lokacin, Comrade Abdulsalam Abubakar Gwarzo ya jagoranci zagayen dubawa a rumfunan nuni domin tantance irin rawar da kowace karamar hukuma ke takawa wajen kare da raya al’adun Hausawa.
Rumfar nuni ta Gwarzo ta jawo hankalin jama’a sosai, inda masu sana’o’i suka gabatar da ayyukansu na gargajiya daban-daban,Mun Sami Zarafin tattaunawa da wasu daga cikin masu sana’o’in domin haskaka gudunmawar su da kwarewarsu.
Ɗaya daga cikinsu, Malam Sani Mai Saka Buli Kare, ya bayyana cewa sana’arsa ta saka an gada ce tun kaka da kakanni. Ya ce ana amfani da bulin da ake sakawa ne musamman a lokutan bukukuwa irin su “Ranar Gada” da “Kauyawa Day”, inda mata ke nuna kyan al’adu da kayan gargajiya.
Haka kuma, Malam Bala Mai Rogo daga Karkari, Madugawa-Gwarzo, ya ce sana’ar sarrafa rogo da gyada ta dade tana zama muhimmin abin dogaro ga al’ummar su, tana taimakawa wajen kula da iyalai da kuma biyan kudin makarantar ‘ya’ya. Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kokarinsa na tallafa wa sana’o’in gargajiya tare da roƙon ci gaba da irin waɗannan shirye-shirye na ƙarfafa masu sana’a.
Shi ma Sulaiman Adamu Usman Gwarzo, wanda shi ne mai fawa (sayar da nama), ya bayyana cewa aikin da suka gada daga iyayensu yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci da aikin yi ga matasa.
A nata jawabin, Hajiya Zulaihat Sabo Usman, Daraktar Mulki da Gudanarwa (DPM), wacce ta wakilci Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho Gwarzo, ta mika godiya ga Gwamnan Jihar Kano bisa shirya wannan gagarumin biki wanda manufarsa ita ce farfaɗo da al’adun Hausawa da kuma karfafawa masu sana’a.
Anasa bangaren Shugaban Sashin walwala da Jin dadin Al-uma na Yankin, Alhaji Abubakar Atiku, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa shi ne irinsa na farko a Jihar Kano da aka kaddamar don tallata al’adun gargajiya.
Ya kuma gode wa Dr. Mani Tsoho Gwarzo, shugaban karamar hukumar, bisa goyon bayansa da jajircewarsa wajen ganin Gwarzo ta fito fili a wannan muhimmin biki.
