News
Lakurawa Sun Kashe Makiyaya 10 A Kebbi
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Bunza da ke Jihar Kebbi sun bayyana cewa mutane goma (10) daga cikin makiyaya Fulani sun rasa rayukansu a harin ramuwar gayya da aka kai musu a kauyen Tilli.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa an kai harin ne bayan da aka kashe wani ɗan sa-kai (vigilante) a yankin, kuma lamarin aka dora laifinsa a kan makiyaya da ke zaune a wajen.
Bayan faruwar lamarin, Shugaban ƙasa na Miyetti Allah tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, sun ziyarci yankin domin mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya ce bai samu cikakken bayani game da lamarin ba, amma ya yi alkawarin bincike da bayar da rahoto daga baya.
