News
Gidauniyar Sallamar Barau Care Foundation Ta Raba Tallafi Ga Mata Marasa Lafiya A Kano
Gidauniyar Sallamar Barau Care Foundation ta gudanar da rabon kayan tallafi ga mata marasa lafiya a asibitin Murtala Muhammad da ke cikin birnin Kano da kuma asibitin Kaura Goje da ke karamar hukumar Nasarawa.
Tallafin ya haɗa da gidan sauro, garin sabulun wanki da kuma kuɗi, kuma an gudanar da shi ne ƙarƙashin jagorancin shugabar gidauniyar, Hajiya Rahama Umar.
Yayin da take jawabi a wajen taron, Hajiya Rahama ta bayyana cewa gidauniyar tana gudanar da irin wannan aiki ne domin taimakon mata musamman masu fama da ƙalubalen tattalin arziki.
“Mun lura cewa mata, musamman iyayen marayu, suna cikin buƙatar taimako a wannan lokaci saboda tsadar rayuwa. Wannan ya sa muka fito da wannan shiri domin rage musu radadi, bisa jagorancin mai girma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin (Maliya),” in ji ta.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin ci gaban yankin Kaura Goje, Alhaji Musa Umar Faruq, ya nuna godiyarsa ga gidauniyar bisa ci gaba da tallafin da take bayarwa a yankin.
“Gidauniyar Sallamar Barau ba yau ta fara aiki ba a wannan yanki. A baya ma ta gyara mana rijiyar burtsatse da ta lalace, yanzu tana aiki sosai. Don haka muna godiya ƙwarai da irin wannan kulawa,” in ji shi.
Wasu daga cikin mata marasa lafiya da suka amfana da tallafin a asibitocin Murtala da Kaura Goje sun bayyana farin cikinsu da wannan taimako, tare da yi wa gidauniyar addu’ar samun lada da ƙarin nasarori a ayyukan alheri.
