Connect with us

News

Wani Fursuna Da Aka Yanke Masa  Hukuncin Kisa Ya Tsere Daga Gidan Yari A Yobe

Published

on

FB IMG 1762007948274

Wani fursuna da aka yanke masa hukuncin kisa, Abba Hassan, ya tsere daga Gidan Gyaran Hali na Tsaro (Maximum Security Custodial Centre) da ke Potiskum, Jihar Yobe, da safiyar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar.

SP Abdulkarim ya bayyana cewa, wanda ya tsere ɗin ɗan asalin Maiduguri ne, Jihar Borno, sannan rundunar ‘yan sanda ta riga ta fara bincike domin gano inda yake da kuma sake cafke shi.

Rundunar ta yi kira ga al’umma, shugabannin gari, direbobi, hukumomin tsaro da kungiyoyin sa kai da su bayar da duk wani bayani da zai taimaka wajen kamo fursunan.

 

 

Advertisement

PLATINUM POST NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending