Connect with us

News

‎Za A Fara Sayar Wani Kofin Kofi Kan Naira Miliyan 1.5 ‎

Published

on

Kofin shayi kofi

Wani gidan shan kofi a birnin Dubai ya fara sayar da kofi guda na haɗaɗɗen kofi a kan kusan Dala 1,000, wato kimanin Naira miliyan 1.5, wanda da haka ya zama mafi tsada a duniya.

‎Gidan shan kofin mai suna Julith Café — da ke cikin unguwar masana’antu da ya zama sabuwar cibiyar masu son kofi, shi ne ya ƙaddamar da wannan sabon nau’in abin sha mai daraja.

Wani Fursuna Da Aka Yanke Masa  Hukuncin Kisa Ya Tsere Daga Gidan Yari A Yobe

‎Ana sa ran gidan shan kofi ɗin zai fara ba da wannan abin sha ga mutane kimanin 400 kacal, ciki har da wani ɗan adadi da aka tanadar wa dangin gidan sarautar Dubai.

‎Wani daga cikin masu mallakar gidan, Serkan Sagsoz, ya ce sun zaɓi Dubai ne saboda “birni ne da ya dace da irin jarin da ke nuna ƙawa da kuma salo.

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending