Connect with us

News

‎Dakarun Soji Sun Halaka ’Yan Bindiga Da Dama, Sun Kwato Babura Kusan 30 A Kano ‎

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Rahotanni daga yankin Farin Ruwa da ke cikin karamar hukumar Shanono a jihar Kano na cewa dakarun sojin Najeriya sun halaka ’yan bindiga da dama tare da kama wasu da ransu, a wani samame da suka kai da daren Asabar.

‎Wani mazaunin garin Goron Dutse, , ya shaida wa Arewa Rediyo cewa sojojin sun kuma kwato babura kusan 30 da ’yan bindigar ke amfani da su wajen kai hare-hare a yankin.

Advertisement

Har Yanzu Ba A San Inda Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Yake Ba

‎A cewar sa, lamarin ya faru ne bayan da ’yan bindigar suka sake kutsawa cikin yankin kamar yadda suka saba yi, sai dai wannan karon dakarun sojin sun yi gaggawar kai musu dauki.

‎“Mun ji karar harbi sosai a cikin dare, daga baya muka ji cewa sojoji sun fatattaki ’yan bindigar. Amma abin bakin ciki, soja daya ya rasa ransa yayin artabu,” in ji mazaunin.

Advertisement

‎Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa jiragen yaki na soji sun shiga yankin cikin dare domin kakkabe sauran ’yan bindigar da suka tsere cikin dazuka.

‎Har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin ba, sai dai mazauna yankin sun bayyana farin ciki da godiya ga yadda dakarun suka mayar da martani cikin gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending