News
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jikkata ‘Yan Sanda Biyu Da Jami’in NSCDC A Yobe
Aƙalla ‘yan sanda biyu da kuma jami’in rundunar Agro Rangers ta Hukumar Tsaro ta NSCDC sun jikkata a wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar Yobe.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kauyen Kojoli da ke karamar hukumar Gulani, inda jami’an suka yi ƙoƙarin hana wasu makiyaya da ake zargi da lalata gonakin shinkafa.
Gwamnan Kano Ya Umarci Shugabannin Ƙananan Hukumomin Jihar Da Su Riƙa Gudanar Da Taron Tsaro
A cewar shaidun gani da ido, maharan sun kai wa jami’an hari da adda, inda suka jikkata su a kai, hannu da ƙafa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa abin ya faru ne a ranar 19 ga Oktoba, bayan samun kiran gaggawa daga mazauna yankin.
“A yayin fafatawar, jami’anmu biyu, Sgt. Abdullahi Aminu da Cpl. Aliyu Suleiman, sun jikkata, inda maharan suka kwace bindigoginsu. Daga baya an dawo da bindiga ɗaya, amma ta ɗaya har yanzu tana hannun waɗanda suka tsere,” in ji DSP Dungus.
DSP Dungus ya ce an tura ƙarin jami’ai zuwa yankin domin tabbatar da tsaro da ci gaba da bincike kan lamarin.
Rikicin manoma da makiyaya na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke barazana ga tsaro da abinci a arewacin Najeriya, musamman a lokutan damina da girbi.
