News
Kano: Matasa 1,654 Sun Ajiye Makamai, Ana Sa Ran Karin 2,100 Sakamakon Shirin Safe Corridor — Waiya
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta samu nasarar saka matasa 1,654 da suka tuba cikin shirin Safe Corridor, domin gyara hali da rage tashin hankali a tsakanin matasa. Ana sa ran karin mutane 2,100 za su shiga shirin nan a makonnin masu zuwa.
Kwamishinan Harkokin Yada Labarai, Comrade Abdullahi Waiya, ya ce an tantance dukkan matasan sosai, kuma sun amince da bin jagorancin gwamnati da wanzar da zaman lafiya.
China Ta Gargadi Amurka Kan Tsoma Baki Cikin Harkokin Najeriya
“Waɗannan matasa sun yi alƙawarin sauya rayuwarsu, su bi hanyar zaman lafiya da aiki mai amfani,” in ji Waiya.
Ya bayyana cewa binciken an gudanar da shi tare da hadin gwiwar Hukumar Leƙen Asirin Jihar (SIB) da jami’an shirin Safe Corridor.
Kwamishinan ya ce shirin ya samo asali ne daga Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ke nuna damuwa kan karuwar tashin hankali tsakanin matasa.
“A karkashin mulkin baya, tashin hankali ya zama sana’a ga wasu. Amma Gwamna Yusuf na kallon matasan a matsayin ‘ya’yansa, kuma ya umurce mu da mu tallafa musu,” in ji Waiya.
Ya ce yawancin matasan da aka hada a shirin suna da baiwa amma ba a yi amfani da ita ba, kuma gwamnati na son dawo da su cikin al’umma domin su zama masu amfani.
Waiya ya kara da cewa:”A baya mun yi hulɗa da 317, a yau mun ƙara 1,654. Nan ba da jimawa ba za mu tantance karin 2,100. Bayan haka za mu mika makamai a hukumance da fara horo.”
Wasu daga cikin matasan za su samu horo kai tsaye tare da NDLEA domin karin tantancewa da tallafi.
Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da Alhaji Aliyu Harazimi da Alhaji Gidado Mukhtar, wadanda suka nuna goyon bayansu ga shirin.
Dan Amar din Kano, Alhaji Aliyu Harazimi, ya bukaci matasan da su dage wajen gudanar da sallah domin hakan zai taimaka wajen kaucewa aikata laifuka, sannan ya roki mawadata da shugabanni su tallafawa yunkurin gwamnati na kawar da harkar daba a jihar.
