News
‘Ba Zan Bar Siyasa Ba Har Tsawon Rayuwata’ — Inji Shekarau Yayin Cikar Sa Shekaru 70
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tshohon Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce siyasa ta zama wani ɓangare na rayuwarsa, kuma ba zai daina shiga harkar siyasa ba muddin yana da ƙarfi da lafiya.
Shekarau, wanda ya cika shekaru 70 a duniya a makon nan, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Kano a wani ɓangare na shagulgulan bikin cikar sa shekaru 70 da haihuwa.
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Matar Da Ta Sace Kanta Don Ta Karbi Kudin Fansa Daga Hannun Mijinta
Ya ce dalilin da yake sa shi ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa shi ne kishin ƙasa da kuma burin ganin an samu shugabanci nagari mai cike da gaskiya da adalci.
“Siyasa wani ɓangare ne na rayuwata. Matukar ina da lafiya da ƙarfi, zan ci gaba da bayar da gudunmawa wajen samar da shugabanni nagari. Ba zan taɓa barin siyasa ba,” in ji shi.
Shekarau ya ce bai taɓa shiga siyasa don neman kuɗi ko matsayi ba, illa kawai don hidima ga jama’a da ƙoƙarin tabbatar da shugabanci mai rikon amana.
“Ba don amfanin kaina na ke siyasa ba. Burina shi ne in tallafa wa shugabanci da ya ginu kan gaskiya da adalci,” in ji shi.
Tsohon gwamnan ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa tsawon rayuwa da Ya ba shi, daga aikin malanta zuwa rike muƙamai daban-daban kamar gwamna, minista da sanata.
“Na gode wa Allah da Ya ba ni damar rayuwa mai tsawo da hidima a fannoni daban-daban. Shekaru 70 a rayuwa babbar ni’ima ce,” in ji shi.
Shekarau ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su rungumi yafiya da zaman lafiya, yana mai cewa ya yafe wa duk wanda ya taɓa ɓata masa rai, tare da neman gafara daga waɗanda shi ma ya ɓata wa rai.
“Na yafe wa duk wanda ya taɓa ɓata min rai, ko na sani ko ban sani ba. Ina roƙon Allah Ya karɓi yafiyata,” in ji shi.
Shekarau, wanda ya mulki Jihar Kano daga 2003 zuwa 2011, ya rike muƙamin Ministan Ilimi a gwamnatin tarayya, sannan ya wakilta ce Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.
Ya gode wa iyayensa, malamai, abokai da magoya bayansa bisa irin rawar da suka taka a rayuwarsa, yana mai cewa zai ci gaba da amfani da rayuwarsa wajen hidima ga al’umma.
“Rayuwa gajeriyar lokaci ce. Kowace rana bayan shekara 70 wata ƙarin ni’ima ce daga Allah, kuma zan yi amfani da ita wajen ci gaba da hidimar ɗan Adam,” in ji shi.
