News
An Ceto Mutum 221 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Jigawa — NAPTIP
Hukumar da ke yaki da fataucin mutane ta kasa (NAPTIP), reshen jihar Jigawa, ta ce ta ceto mutum 221 da suka fada hannun masu safarar bil-adama a cikin shekaru biyu.
Kwamandan hukumar a jihar, Malam Abdulladir Turajo, shi ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin wani taron wayar da kan jama’a da aka yi a garin Kazaure.
Rasha Ta Ce Tana Sa Ido Kan Nijeriya Bayan Barazanar Da Trump Ya Yi Ta Kai Hari Kasar
Turajo ya ce tun bayan kafa ofishin hukumar a Jigawa a watan Yulin 2023, aka samu nasarar ceto wadannan mutane, inda aka kammala bincike tare da mayar da su hannun iyalansu lafiya.
Ya kuma ce a cikin wannan lokaci, hukumar ta:
Samar da hukuncin kotu kan mutum biyu da aka kama da laifin safarar mutane, Gabatar da shirye-shiryen wayar da kai 175, Gudanar da fadakarwa a makarantu, masallatai, majami’u, kasuwanni, da tashoshin ababen hawa
An shirya gangamin ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Cigaban Al’umma ta jihar Jigawa.
Turajo ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bada hadin kai, musamman wajen kai rahoton duk wani abu da ya shafi wannan aika-aika, domin kare matasa da yara daga fadawa hannun ’yan safara.
