Connect with us

News

Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 12 Tare Da Jikata 27 A Pakistan

Published

on

Suicide explosion

A kasar Pakistan an kaddamar da bincike bayan hukumomin sun tabbatar da wani harin kunar bakin wake, a kofar ofishin ‘yan sanda na birnin Islamabad wanda ya janyo halaka mutane 12.

Wani harin kunar bakin wake a kofar ofishin ‘yan sanda da ke birnin Islamabad fadar gwamnatin kasar Pakistan ya halaka mutane 12.

Advertisement

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Ofishin Kwastam A Kebbi

Ma’aikatar cikin gida ta tabbatar da faruwan lamarin inda kuma wasu mutanen 27 suka jikata. Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Hukumomin kasar ta Pakistan sun kwashe watanni suna neman hanyoyin dakile tashe-tashen hankula masu nasaba da tsagerun Taliban masu dauke da makamai a kasar.

Advertisement

Firaminista Shehbaz Sharif ya yi tir da hare-haren da ake fuskanta a kasar, yayin da hukumomi ke kara kaimin magance wannan matsalolin da Pakistan ke fuskanta.

 

Advertisement

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending