News
NSCDC Ta Karrama Ma’aikacin Wucin Gadi da Ya Mayar Da Naira Miliyan 20 Da Ya Tsinta A Kano
Rundunar Tsaron Civil Defence ta Najeriya (NSCDC) ta shiyyar 12 ta karrama wani ma’aikacinta na wucin gadi, Nura Abdullahi, bayan ya mayar da kimanin Naira miliyan 20 da ya tsinta a cikin wani adaidaita sahu a Kano.
A cewar rundunar, Nura ya gano kudin ne a lokacin da ya hau adaidaita sahu, inda daga nan ya koma wajen jami’an NSCDC domin neman yadda za a gano mamallakin kuɗin, da daga bisani aka tabbatar shi ne wani ɗan kasuwa daga Katsina, Alhaji Mustafa, wanda ya zo Kano domin harkar kasuwanci.
Gwamnan Kano Zai Gabatar Da Kasafin 2026 Da Ya Haura Naira Tiriliyan Daya Ga Majalisar Dokokin Jihar
Da yake mika masa takardar yabo a madadin babban kwamandan rundunar na kasa, Ahmad Audi, kwamandan shiyyar Kano da Jigawa, ACG Amos Abiodun Taiwo, ya bayyana abin da Nura ya aikata a matsayin abin koyi da ake bukatar sauran ‘yan Najeriya su yi koyi da shi.
Ya ce irin wannan ɗabi’ar na nuna cewa akwai mutane masu rikon amana a cikin al’umma, lamarin da ya kara ɗaga martabar rundunar a idon jama’a.
“Ba wai mayar da kuɗi kaɗai muke yabawa ba, amma saboda nuna cewa gaskiya da amana har yanzu suna da muhimmanci a tsakanin jama’a,” in ji ACG Taiwo.
A nasa bangaren, mamallakin kuɗin Alhaji Mustafa ya bayyana cewa mayar masa da kuɗin ya zama babban taimako gare shi, yana mai godewa rundunar da kuma Nura kan abin da ya kira “taimakon da ya ceci rayuwa”.
