Connect with us

News

Rundunar Sojin Najeriya Ta Cafke Wani Da Ake Zargin Mai Garkuwa Da Mutane A Taraba

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Rundunar sojin Najeriya ta cafke wani da ake zargin mai garkuwa da mutane, Umar Musa Geyi, a karamar hukumar Wukari yayin da yake tattaunawa kan kudin fansa na Naira miliyan 20 daga dangin wani da aka sace.

‎Kakakin rundunar, Laftanar Umar Mohammed, ya ce wanda ake zargin yana cikin jerin wadanda hukumomin tsaro ke nema, kuma yana da hannu a sace Alhaji Jano, wani Bafulatani mazaunin Jandei-Kulala, wanda aka sace ranar 13 ga Nuwamba, 2025.

Advertisement

Kare Kai Da Al’ummomi Ke Yi Ne Ke Kara Haifar Da Sabbin Rikice-rikice A Filato – Sojin Najeriya

‎“Laftanar Mohammed ya ce: ‘Binciken farko ya nuna wanda ake zargin yana da alaka da sace Alhaji Jano, kuma har yanzu yana hannun masu garkuwa.’”

Advertisement

‎Ya kara da cewa wanda ake zargin an kama shi ne yayin da ake tattaunawa da dangin wanda aka sace a kan kudin fansa na Naira miliyan 20, sannan yana hannun jami’an tsaro yanzu ana ci gaba da yi masa tambayoyi domin gano inda wanda aka sace yake.

‎Kwamandan 6 Brigade, Brigade General Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa sojojin kan jajircewa da kwarewarsu, tare da tabbatar da cewa rundunar tana ci gaba da yaki da duk wata kungiyar masu laifi a fadin jihar.

Advertisement

‎Rundunar ta ce za ta ci gaba da bincike domin kamo sauran da ke da hannu a wannan lamarin, tare da tabbatar da cewa wanda aka sace zai dawo hannun iyalansa lafiya.

Advertisement

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending