News
Jami’an Soji Sun Kama Wani Gawurtaccen Mai Garkuwa Da Mutane A Taraba
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kama wani da ake zargi babban jagoran masu garkuwa da mutane a kudancin Jihar Taraba.
A cewar rundunar, an kama wanda ake zargin, Abubakar Bawa, ne a ranar 23 ga Nuwamba 2025 a karamar hukumar Wukari, bayan samun bayanan leƙen asiri da suka nuna yana ƙoƙarin tserewa daga yankin.
Umarnin Janye ’Yan Sanda Daga Gadin Manyan Mutane Na Iya Zama Magana Kawai —Shehu Sani
Sojojin 6 Brigade/Sector 3 ƙarƙashin Operation Whirl Stroke ne suka aiwatar da kamen.
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa Bawa na da alaƙa da Umar Musa, wani fitaccen mai garkuwa da rundunar ta kama a ranar da ta gabata, 22 ga Nuwamba.
Binciken farko, a cewar rundunar, ya nuna cewa mutanen biyu na cikin wata babbar ƙungiyar laifi da ake zargin tana da hannu a garkuwa da mutane, hare-haren bindiga da sauran laifuka a yankin kudancin Taraba.
Kwamandan 6 Brigade/Sector 3 OPWS, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya bayyana kamen a matsayin muhimmiyar nasara ga aikin da rundunar ke yi.
Wasu mazauna Wukari sun shaida cewa kama waɗannan mutane biyu cikin kwanaki ya samar da ɗan natsuwa a yankin, musamman ganin yadda hare-haren baya-bayan nan ke barazana ga rayuwar jama’a.
