News
Jihar Gombe Ta Rufe Dukkan Makarantu Sakamakon Ƙaruwar Matsalar Tsaro
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayar da umarnin a rufe dukkan makarantu na jihar daga yanzu zuwa ranar Juma’a, 28 ga Nuwamba, sakamakon ƙaruwar matsalar tsaro.
Shugaban Hukumar SUBEB ta jihar, Dr. Esrom Toro, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da Sakataren Ilimi na kananan hukumomi a hedikwatar hukumar da ke Gombe.
Dakarun Soji Sun Cafke Wani Fitaccen Mai Garkuwa Da Mutane A Taraba
Toro ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan ƙarin tashin hankali da hare-hare kan makarantu a Arewa, ciki har da sace-sacen ɗalibai da ya sake ƙaruwa a jihohin arewacin ƙasar nan.
Ya ce: “Gwamna Inuwa Yahaya ya umarci cewa dukkan makarantu su rufe daga yanzu zuwa ranar Juma’a. Wannan mataki ne na kariya domin tabbatar da lafiyar ɗalibai, malamai da ma’aikatan makarantu.”
“Muna kira ga iyaye su kwantar da hankalinsu. Gwamnati na aiki tuƙuru wajen dakile barazanar tsaro da kare rayukan al’ummar Gombe,” in ji shi.
Sace ɗalibai 303 da malamai 12 daga makarantar St. Mary’s, Papiri, a Jihar Neja — 21 ga Nuwamba, 2025.
Sace ’yan mata 25 a Kebbi, inda aka kashe mataimakin shugaban makarantar lokacin harin.
A sakamakon haka, gwamnati ta tura umarnin rufe makarantu 47 na Unity Schools, yayin da jihohin Katsina da Bauchi suma suka rufe wasu makarantunsu na wucin-gadi saboda barazanar tsaro.
