News
Kotu Ta Yanke Wa Magidanci Hukuncin Daurin Shekara Daya Saboda Satar Wake kwano Daya
Wata kotu a Jihar Adamawa ta yanke wa Iliya Abdullahi, wani magidanci daga Karamar Hukumar Shelleng, hukuncin daurin shekara guda a gidan yari saboda satar mudu ɗaya na wake.
Rahotanni daga Daily Trust na nuna cewa, tun farko kotun Lamba 2 ta Shelleng ta yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan yari, bisa laifin da ya saɓa wa Sashe na 277 na Kundin Penal Code. An tura shi gidan yari ne a ranar 15 ga Nuwamba, 2025.
Jihar Gombe Ta Rufe Dukkan Makarantu Sakamakon Ƙaruwar Matsalar Tsaro
Daga bisani, Shugabar Kwamitin Gudanar da Gidajen Yari (JDC) kuma Shugabar Kotun Jihar, Justice Hafsat Abdulrahman, ta sake duba hukuncin. Ta rage masa hukuncin daga shekaru biyu zuwa shekara guda lokacin ziyarar da kwamitin ta kai Shelleng Satellite Custodial Centre ranar Laraba.
Justice Abdulrahman ta shawarci Abdullahi da ya zama mai kyawawan halaye kuma ya bada gudummawa ga ci gaban al’umma.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
