News
’Yan Bindiga Sun Sace Mata 10 A Kano
Wasu ’yan bindiga sun kai hari a garin ’Yan Cibi da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta jihar Kano, inda ake zargin sun sace mata 10 a daren jiya.
Wani mazaunin garin da ya yi magana da Freedom Radio ya ce maharan sun shigo garin ne da misalin karfe 10 zuwa 11 na dare, a kan babura sama da 30. Ya ce maharan sun yi garkuwa da ’yan mata da kuma matan aure, abin da ya kara tsananta fargaba a yankin.
Kotu Ta Yanke Wa Magidanci Hukuncin Daurin Shekara Daya Saboda Satar Wake kwano Daya
A cewar mazaunin garin, tun kafin wannan harin, al’ummar garin sun jima suna rayuwa cikin zaman dar-dar, inda maza da dama ke yin barci a kan bishiyoyi, ko kuma a waje nesa da gidajensu, saboda yawan hare-haren da ake kaiwa a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shigo garin ne , yankuna da ke iyaka da Yar Gajam a Karamar Hukumar Musawa ta jihar Katsina, kafin su kutsa cikin ’Yan Cibi.
Hukumomi dai ba su fitar da wata sanarwa game da harin ba tukuna, kuma ana jiran karin bayani daga hukumomin tsaro.
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News15 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
