News
Gwamnatin Kano Za Ta Hukunta Duk Wanda Aka Samu Na Amfani Da Babur Mai Kafa 2 Da Nufin Achaba
Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta hukunta duk wani mutum da aka kama yana gudanar da sana’ar achaba a cikin birnin Kano da kewaye, duk da haramcin da aka dade da kakabawa wannan kasuwanci.
Hakan na zuwa ne bayan da rahotanni suka nuna cewa masu babur mai kafa biyu sun fara sake bayyana a titunan Kano, lamarin da ya haifar da ƙarin damuwa a tsakanin jama’a da hukumomi.
A cikin wani saƙon manema labarai da Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta jihar ta fitar, gwamnatin ta tabbatar da cewa rahotannin leƙen asiri sun nuna akwai yawaitar masu babur, har ma da wasu mutane ba a san su ba da ke shigowa unguwanni suna zirga-zirga da babura da sunan achaba.
Gwamnatin ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro domin dakile wannan matsala a kananan hukumomi 44 na jihar.
“Duk wanda aka kama yana yin achaba a Kano, babu shakka zai fuskanci hukuncin doka.”
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
