Connect with us

News

Rundunar Sojin Sama Ta Tarwatsa Sansanonin Ƴan Ta’adda A Katsina Da Borno

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta gudanar da jerin hare-hare a jihohin Katsina da Borno, lamarin da ya yi sanadin tarwatsa sansanonin ƴan ta’adda da hana wani gagarumin hari na ISWAP/Boko Haram samun nasara a Chibok.

Rundunar ta ce a Jihar Katsina, dakarunta sun kai hare-hare guda biyu a ranar 27 ga Nuwamba 2025 ƙarƙashin OPERATION FANSAN YAMMA (OPFY) Sector 2. Harin farko ya auku da misalin ƙarfe 6:30 na safe, inda jiragen yakin NAF suka kai farmaki kan sansanin wani sanannen jagoran ta’addanci da ke da hannu a garkuwa da mutane da kai hare-hare a Kankara, Faskari da Malumfashi.

Advertisement

Gwamnatin Kano Za Ta Hukunta Duk Wanda Aka Samu Na Amfani Da Babur Mai Kafa 2 Da Nufin Achaba

An kai wa sansanin Harin inda aka kashe su sannan aka ci gaba da bibiyar waɗanda suka arce ana yi musu luguden wuta.

Daga bisani, da misalin ƙarfe 5:55 na yamma, jiragen NAF suka sake kai hari a Danfako, Faskari LGA, inda suka tarwatsa wasu manyan sansanonin ƴan ta’adda da cibiyoyin kayayyaki, ginin da suke amfani da shi, da kayan aikinsu. An kashe ƴan ta’adda da dama, lamarin da ya dakushe karfin yanayin hare-harensu a yankin Arewa maso Yamma.

Advertisement

A Jihar Borno kuwa, sojojin Rundunar 28 Task Force Brigade na OPERATION HADIN KAI (OPHK) tare da hadin guiwar mayakan sama sun dakile wani babban hari da ƙungiyoyin ISWAP/Boko Haram suka ƙaddamar a Chibok.

Jiragen NAF sun kai hare-hare huɗu, bisa bayanan da suka samu daga sojojin ƙasa, kan mayakan da suka fara ja da baya bayan an tarwatsa su. Karin hare-hare kan waɗanda ke gudu ya tabbatar da cewa ba su sami damar sake haduwa ba don kai wasu hare-haren.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa haɗin gwiwa tsakanin sojojin sama da na ƙasa ya kare al’ummar Chibok, tare da hana mayakan ISWAP damar samun nasarar kai hari ko sake dawowa da karfi.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce za ta ci gaba da kai hare-haren da suka dace da kare rayukan ‘yan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.

Advertisement

 

 

Advertisement

Premium times

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending