Connect with us

News

Ɗalibi Ya Rasa Ransa A Hatsarin Mota Yayin Murnar Kammala Jarabawa A Jami’ar AAU

Published

on

Motar da ta yi hatsari

Wani ɗalibi na shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli (AAU), jihar Edo, ya rasa ransa a wani hatsarin mota yayin da shi da wasu abokan karatunsa ke gudanar da jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe.

Majiyar gidan yanar gizo mai suna Inside Edo ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne ranar Litinin, jim kaɗan bayan daliban sun kammala jarabawar ƙarshe, sai dai har yanzu ba a bayyana sunan ɗalibin da ya rasu ba.

Advertisement

’Yan Najeriya 32  Aka Kora Daga Indiya Kan Tuhumar Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Majiyar ta ce, “Motar ɗalibin ta yi ƙoƙarin wuce wata mota, sai ta kwace ta kuma ta buge wata babbar mota da ke tsaye a hanya. Wannan ya haifar da mutuwar ɗalibin nan take.”

Wani jami’in da ya ga abin da ya faru ya ce, “Mazauna yankin Ujoelen, kusa da makarantar firamare, sun ruga wurin, amma ba a iya ceto wanda ya jikkata ba. Hatsarin ya faru ne yayin yunƙurin wucewa da ɗaya daga cikin motocin da ke cikin jerin gwanon.”

Advertisement

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa hatsarin ya faru ne yayin da ɗaliban ke tukin mota cikin ganganci, sun yi yunƙurin taho-mu-gama da wata babbar mota da ke tsaye a hanya.

Kwamandan sashe na Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC) a jihar Edo, Cyril Mathew, ya tabbatar da lamarin ga NAN, inda ya ce mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu biyar suka jikkata. Ya ce:

Advertisement

“Bayan sun kammala rubuta takardar jarabawar ƙarshe, ɗaliban sun shiga jerin gwanon motoci a hanya. A yayin wannan gasa, ɗaya daga cikinsu ya yi yunƙurin wuce wata mota, amma sai ya buge da wata babbar mota da ke tsaye a gefen hanya, wanda ya jawo mutuwar ɗalibin.”

Hukumar FRSC ta yi kira ga ɗalibai da su guji irin wannan gasa a hanyoyi domin kare rayukansu da na sauran masu ababen hawa a hanya.

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending