Connect with us

News

‎Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Jariri Dan Wata 8 Da Wata Mata‎

Published

on

IMG 20251214 WA0009

Jariri mai watanni takwas a Duniya da wata mata sun rasu sakamakon hatsarin mota da ya auku a kan titin Ikorodu da ke jihar Legas, bayan taho-mu-gama tsakanin bas biyu na sufuri a safiyar Lahadi.

‎Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kusa da Olabode House, tsakanin Anthony da Obanikoro.

Advertisement

Wasu Bata-gari Sun Hallaka Wata Mata Mai Juna Biyu Da Ɗanta A Kano  ‎

‎A cewar hukumar, wata bas ja kirar Tata da ke tafiya daga Palmgroove zuwa Anthony ta rasa iko, ta ketare shingen tsakiyar hanya, sannan ta bugi wata bas kirar Volkswagen da ke kan hanyar Palmgroove.

‎Hukumar  ta ce matar ta rasu nan take a wajen hatsarin, yayin da jaririn mai watanni takwas ya rasu daga baya sakamakon munanan raunukan da ya samu.

Advertisement

‎Rahoton ya kara da cewa wasu mutane 10, ciki har da direbobin motocin biyu, sun jikkata da raunuka daban-daban.

An ceto fasinjoji shida daga bas din Volkswagen, yayin da aka kubutar da mutane hudu daga bas din Tata.

Advertisement

‎Jami’an LASTMA, tare da hadin gwiwar jami’an agajin gaggawa da mazauna yankin, sun killace wurin hatsarin tare da kwashe motocin da suka lalace domin kauce wa karin hatsari da kuma dawo da zirga-zirgar ababen hawa a kan babbar hanyar.

‎Hukumar Kula da Jinyar Gaggawa ta Jihar Legas (LASAMBUS) ce ta dauki wadanda suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawar lafiya, yayin da jami’an kula da lafiyar muhalli suka kwashe gawarwakin mamatan.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

THECABLE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending