News
Gobara Ta Tashi A Ofishin FIRS
Wata gobara ta tashi a ɗaya daga cikin ofisoshin hukumar karɓar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa (FIRS) da ke Abuja a yau Asabar.
Wani bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna wutar tana ƙone wasu sassan ginin, lamarin da ya jawo firgici a yankin.
Dakarun Soji Sun Cafke Motocin A-kori-kura Biyu Ɗauke Da Kayayyaki Na ‘Mayaƙan ISWAP’
A cikin wata sanarwa da Sikiru Akinola, jami’i a fannin yada labrai na hukumar FIRS ya sanya wa hannu, hukumar ta ce gobarar ta tashi ne a ofishinta da ke Lamba 15, titin Sokode Crescent, Wuse Zone 5.
“Gobarar, wadda ta tashi a bene na huɗu na ginin, jami’an tsaronmu da ke bakin aiki sun ɗauki mataki cikin gaggawa,” in ji sanarwar.
“Da saurin tallafin hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya da sauran jami’an agajin gaggawa, an samu nasarar shawo kan wutar tare da hana ta yaɗuwa zuwa wasu sassa.”
-
News2 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News17 hours ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Tsawaita Dakatarwar Da Ta Yi Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomin Rogo, Bagwai Da Bebeji

