Connect with us

News

Jami’ar MAAUN Ta Karrama Marigayi Janar Abacha Da Baré Maïnassara Da Digirin Girmamawa

Published

on

FB IMG 1766343346833

Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) da ke Kano ta bai wa tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Marigayi Janar Sani Abacha, da kuma tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar, Marigayi Ibrahim Baré Maïnassara, digirin girmamawa na Doctor of Leadership bayan rasuwarsu.

An ba da karramawar ne a yayin bikin yaye dalibai na farko na jami’ar, wanda aka gudanar a harabar jami’ar a ranar Asabar.

Advertisement

Gobara Ta Tashi A Ofishin FIRS

Alhaji Mohammad Sani Abacha ne ya karɓi digirin a madadin marigayi Janar Abacha, yayin da Dr. AbdulRasheed Amadu ya karɓa a madadin marigayi Baré Maïnassara.

Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ce an karrama shugabannin biyu ne bisa rawar da suka taka wajen jagoranci da ci gaban ƙasashensu.

Advertisement

Farfesa Gwarzo ya ce a lokacin mulkinsa, Janar Abacha ya nuna tsayayyen shugabanci da jajircewa wajen tabbatar da kwanciyar hankali, tare da aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa, musamman ta hannun Petroleum (Special) Trust Fund (PTF).

A cewarsa, PTF ta aiwatar da ayyuka a fannonin gine-ginen hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi, ruwan sha da sufurin jama’a, musamman a yankunan karkara.

Advertisement

Game da Marigayi Baré Maïnassara, jami’ar ta ce tsohon shugaban na Nijar ya taka rawa wajen ƙarfafa haɗin gwiwar yankin Yammacin Afirka, musamman a fannin tsaro a wani lokaci da yankin ke fuskantar ƙalubale.

Da yake jawabi a madadin iyalan Abacha, Alhaji Mohammad Sani Abacha ya gode wa jami’ar, yana mai cewa karramawar na nuna amincewa da gudunmawar da marigayi Janar Abacha ya bayar ga ƙasa da ilimi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending