News
MAAUN Ta Ba Dalibai 43 Masu First Class Guraben Karatun A Ƙasashen Waje
Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) ta ba wa dalibai 43 da suka kammala karatu da digiri na First Class guraben karatun ƙasashen waje domin yin digiri na biyu, a bikin yaye dalibanta na farko da aka gudanar a ranar Asabar a Kano.
Wanda ya kafa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ce guraben karatun za su ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen karatun Master’s degree a kowace ƙasa da ɗaliban suka zaɓa.
Jami’ar MAAUN Ta Karrama Marigayi Janar Abacha Da Baré Maïnassara Da Digirin Girmamawa
Ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da su kasance jakadun na gari ga jami’ar, tare da wakiltar martabar ilimi da nagartar ɗabi’a a duk inda suka je.
A nasa jawabin, shugaban jami’ar, Farfesa (Dr.) Mohammed Israr, ya ce MAAUN ta fara ayyukan karatu a 2022 da shirye-shirye 15 a makarantu huɗu, amma yanzu ta faɗaɗa zuwa shirye-shirye 22 a makarantu takwas.
Ya ce jami’ar ta samu matsayi na biyu a cikin jami’o’in masu zaman kansu a Najeriya, kamar yadda AD Scientific Index ta bayyana, wannan alamar jajircewa wajen inganta ilimi.
A cewarsa, dalibai 492 ne suka kammala karatu daga shirye-shirye 12, inda 43 suka samu First Class, 220 suka samu Second Class Upper, yayin da 229 suka kammala da Second Class Lower.
Da yake jawabi a bikin, Chancellor na jami’ar, Farfesa Mahamouda Salouhou, ya ƙarfafa wa daliban gwiwar kiyaye ƙa’idoji da martabar jami’ar.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda shugaban ma’aikatansa, Dakta Wali Sulaiman Sani, ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa fannin ilimi.
Dalibar da ta fi kowa kwazo, Khadija Ibrahim Manzo daga sashen Human Resource Management, ta samu kyautar Naira miliyan 5 daga wanda ya kafa jami’ar.
Bikin yaye daliban ya samu halartar shugabannin jami’o’i, sarakunan gargajiya da manyan jami’an gwamnati daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
