Connect with us

Business

Farashin Man Fetur Zai Iya Haura N1,400 Idan Nijeriya Ta Dogara Da Shigo Da Mai Daga Waje — Dangote

Published

on

Dangote Refinery Loading Bay
Spread the love

Matatar man fetur ta Dangote ta yi gargaɗin cewa farashin litar fetur a Nijeriya na iya haura N1,400 idan har ƙasar ta koma dogaro kacokan da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Matatar ta bayyana cewa samar da mai a cikin gida ya zama muhimmin ginshiƙi wajen daidaita farashi da hana tashin gwauron zabi a kasuwar man fetur ta Kasar.

‎Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabbin Dabaru Domin Dakile Satar Amsa A Jarabawar WAEC Da NECO

Dangote Refinery ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, inda ta karyata rahotannin da ke cewa za ta dakatar da aiki domin gyara, tana mai cewa rahotannin ƙarya ne kuma an yaɗa su da gangan domin ba da hujjar ƙara farashin fetur.

A cikin wata sanarwa, matatar ta ce idan ba don aikin ta ba, masu shigo da mai daga waje za su ci gaba da yin abin da suka ga dama, lamarin da zai iya kai farashin fetur zuwa  N1,400 kan kowace lita.

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa ayyukan matatar Dangote sun zama ginshiƙi na daidaita kasuwar man fetur, tare da rage tasirin masu shigo da mai da ke neman riba ba tare da la’akari da halin da jama’a ke ciki ba.

 

PUNCH

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *